in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Angola ya yi kira kan yin shawarwari domin warware rikicin yankin Grands Lacs
2014-01-16 15:27:56 cri

A ranar 15 ga wata, shugaban kasar Angola José Eduardo dos Santos ya bayyana cewa, ya kamata kasashen da ke yankin Grands Lacs su warware rikicin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, ta yadda za'a cimma burin samar da dauwamammen zaman lafiya a wannan shiyya.

A gun taron koli na kungiyar kasa da kasa karo na biyar na yankin Grands Lacs da aka yi a birnin Luanda, hedkwatar kasar Angola, mista Santos ya nuna cewa, yanzu ana samun matsala sosai a yankin Grands Lacs, ana cigaba da samun zaman dar dar da rikici a yankin gabashin Kongo(Kinshasa), da Sudan ta Kudu, da Afrika ta tsakiya, ya kuma bayyana fatansa na ganin taron ya samar da wani dandalin tattaunawa domin warware rikicin da shiyyar take fama da shi. Kasashen da ke halartar taron sun yaba wa kokarin da kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da AU suka yi wajen warware rikicin kasar Sudan ta Kudu da neman samun sulhunta kabilun dake gaba da juna.

Shugaban Dos Santos ya bayyana cewa, ya kamata kasashen da ke yankin Grands Lacs su dukufa ka'in da na'in wajen shimfida tsarin demokuradiyya da raya zamantakewar al'umma, da kafa dangantakar sada zumunta da kasashe makwabta, don ba da tabbaci ga aikin samar da zaman lafiya da karko a wannan yankin. A sa'i daya kuma, ya yi kira ga kasashen daban daban da su yi kokari wajen yaki da talauci, cututtuka, tare da sa kaimi ga gudanar da harkokin iyakokin kasashen dake wannan shiyya, kana da tabbatar da raya tattalin arziki ta hanyoyi da dama, da kuma yaki da ta'addanci.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China