Madam Hua wadda ta bayyana hakan a wajen taron manema labarai, tace bayan samun labarin kame 'yan kasashen waje da yawa a Angola, ciki har da Sinawa, ma'aikatar harkokin waje ta Sin da ofishin jakadancin Sin a Angola sun bukaci mahukuntan Angola da su tabbatar da iko da moriyar Sinawa a wurin bisa doka, sannan su daidaita wannan batu cikin sauri bisa doka yadda ya kamata.
Kakakin ta kara da cewa, gwamnatin kasar Sin bata amince da kowane irin danyen aiki na keta doka ba, kuma za ta ci gaba da bukatar Sinawa dake Angola da su bi doka a wurin, su ba da kariya ga yanayin da ake ciki na samun moriyar juna.
An bada labarin cewa, a ranar Jumma'a 19 ga wata, a kokarin yaki da bakin haure da masu neman aikin yi ba bisa doka ba, 'yan sandan kasar ta Angola sun gudanar da samame a birnin Luanda, hedkwatar kasar, inda suka kame 'yan kasashen waje sama da dubu daya, ciki har da Sinawa sama da 300, wadanda suke aiki da kasuwanci a can. Bisa kokarin ma'aikatar harkokin waje ta Sin da na ofishin jakadanci na Sin a Angola, a ranar lahadin nan an saki yawancin Sinawa da 'yan sandan suka kame amma ba tare da dogon bincike ba. sai dai kawo yanzu ana ci gaba da tsare sauran Sinawa sama da 30 a sakamakon rashin samun izini.(Fatima)