Layin dogo na Benguela mai tsawon kilomita 1344 ya tashi ne daga birnin Lobito mai tashar jiragen ruwa dake kusa da tekun Atilantika, har zuwa birnin Luau dake iyaka da kasar Congo-Kinshasa, kana muhimmiyar hanyar kasuwanci ga Lobito na kasar Angola.
Wasu masana na ganin cewa, layin dogon Benguela zai taimaka matuka ga kasashen Congo-Kinshasa, Zambia da sauransu wajen rage kudin da za su kashe kan fitar da ma'adinai. A sa'i daya kuma, bayan hade wannan layin dogon da layoyin dogo na kasashen Zimbia, Congo-Kinshasa, Mozambique da dai sauran kasashen dake kewayensa, zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arzikin yankin, tare da kafa wani babban layin dogo dake tsakanin tekun Atilantika da tekun India. (Maryam)