Rahotanni daga kasar ta Angola sun bayyana cewa, jirgin dake wa tawagar jagora mai taken 'Yancheng' ya bar gabar ruwan Luanda da misalin karfe 4 na yamma bisa agogon kasar, a hanyar sa zuwa kasar Namibia, domin ci gaba da ziyarar sada zumunta a kasashen Afirka. Sauran jiragen dake cikin wannan tawagar sun hada da Luoyang da Taihu.
Yayin wannan ziyara dai shugaban tawagar Li Chengpeng, ya gana da mahukuntan Angola a birnin Luanda, da manyan jami'an rundunar ruwan kasar, tare da musayar ra'ayi da takwarorin tawagar na Angola.
Manyan jami'ai da suka hada da manzon kasar Sin a kasar Gao Kexiang, da wakilan rundunar ruwan kasar, da kuma daruruwan Sinawa dake kasar ne suka isa gabar ruwan ta Luanda domin ban kwana da tawagar sojojin ruwan kasar Sin.(Saminu Alhassan Usman)