in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samarwa Nepal tallafin kayayyaki da ya kai kudin Sin RMB miliyan 60
2015-05-07 21:06:24 cri

Mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin Qian Keming ya yi bayani a wani taron manema labaru da aka yi a yau Alhamis 7 ga wata cewa, bayan aukuwar girgizar kasa a kasar Nepal, ma'aikatarsa ya yi hadin kai da sauran hukumomin kasar Sin don baiwa kasar Nepal kayayyakin agaji ciki gaggawa har sau biyu. Kuma wadannan tallafin kayayyaki da Sin ta samar kimanin tan 546 ya kai kudin Sin RMB miliyan 60.

Qian Keming a cewarsa, baiwa kasashen waje tallafin jin kai yayin da suke fama da bala'u wani muhimmin mataki ne da Sin take dauka. Tun daga farkon shekarar 2014 zuwa yanzu, Sin ta bayar da agajin jin kai da ya kai kudin Sin biliyan 1.3 ga kasashe kimanin 40 daga nahiyoyin Asiya, Afrika, da kuma Oceania. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China