in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin bada ceto na Sin ya fara gyara hanyoyin mota dake kasar Nepal
2015-05-05 11:07:17 cri
A jiya Litinin ne da karfe 9 da safe, rukunin kula da aikin sufuri na 'yan sanda masu dauke da makamai na kasar Sin ya fara ayyukan farfado da sufuri a kasar Nepal. A sakamakon wannan girgizar kasa, hanyoyin mota da gine-gine sun lalace sosai a kasar, wannan ya sa ayyukan rukunin ke fuskantar tafiyar hawainiya.

Bisa bukatun da kasar Nepal ta bayar, a ranar 3 ga wata ne, gwamnatin kasar Sin ta tura rukunin sufuri na 'yan sanda masu dauke da makamai zuwa kasar Nepal don bada gudummawa wajen farfado da harkokin sufuri a kasar. Tawagar farko ta rukunin dake kunshe da mutane kimanin 160 sun iso kasar Nepal, kuma babban aikin da ke gabansu shi ne gyara hanyoyin mota dake tsakanin Sin da Nepal.

Ban da wannan kuma, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon girgizar kasar da ta faru a kasar Nepal ya ci gaba da karuwa. Ya zuwa daren ranar 4 ga wata, gwamnatin kasar Nepal ta sanar da cewa, mutane 7365 sun mutu yayin da mutane 14355 suka ji rauni a sakamakon bala'in. Kana rukunin bada ceto ya gano gawawwaki fiye da dari daya a wani kauye da zabtarewar dusar kankara ta binne su. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China