in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakiyar babban magatakardan MDD ta jinjinawa kwazon ayyukan ceto da ba da jinya na Sin a Nepal
2015-05-04 09:44:54 cri
Tun loacin da tawagar Red Cross ta kasar Sin ta isa kasar Nepal a ran 30 ga watan Afrilu, ya zuwa yanzu, tawagar ta ba da jinya ga mutane sama da dari shida, galibinsu mata ne da kananan yara.

A ko wace rana, tawagar ta kan yi tattaki da mota zuwa yankunan karkara domin ba da jinya, a sa'i daya kuma, tawagar ta kula da aikin kandagarkin barkewar cututuka masu alaka da bala'in girgizar kasar, sa'an nan kuma, tawagar za ta fara aikin ilimantar da jama'a kan harkokin kiwon lafiya.

Kaza lika, bisa gayyatar da hukumar ceto ta kasar Nepal ta yi wa gwamnatin kasar Sin, wata tawagar musamman mai kunshe da mutane shida ta tashi daga babban birnin kasar Nepal, Katmandu zuwa lardin Sindhupal chowk ta jirgi mai saukar ungulu inda bala'in ya fi shafa sosai domin fara aikin kandagarkin barkewar cututuka masu alaka da bala'in girgizar kasar.

Bugu da kari, a ran 2 ga wata, mataimakiyar babban magatakardan MDD mai kula da harkokin jin kai na MDD, kana jami'ar kula da aikin ceton gaggawa Valerie Amos ta jinjinawa kwazon ayyukan ceto da ba da jinya da kasar Sin ta yi a kasar Nepal.

Kana, yayin da take tsokaci kan yanayin da kasar Nepal take ciki, Madam Amos ta ce, a halin yanzu, jama'ar kasar da bala'in ya shafa na bukatar wuraren zama da kuma ruwan sha. Haka kuma ta ce, asusun kula da ayyukan gaggawa na MDD ya sanar da samar da dallar Amurka miliyan 15 domin taimakawa aikin ceto, kana a halin yanzu, akwai tawagogin aikin ceto 62 da suka zo daga kasashen ketare da kuma tawagogin ba da aikin ceto 75 da suke gudanar da ayyuka a kasar Nepal. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China