in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon firaministan Nepal ya godewa gwamnatin Sin bisa taimakon da ta baiwa kasar sa
2015-05-03 16:19:23 cri
Tsohon firaministan Nepal, Puspa Kamal Dahal Prachanda, ya jinjinawa gwamnati da jama'ar kasar Sin, bisa taimakon da suka baiwa kasar sa, biyowa bayan bala'in girgizar kasa mai karfi da ta aukawa kasar a ranar 25 ga watan Afrilun da ya gabata.

Prachanda ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin da yake zantawa da kafofin yada labaru na Sin.

A wani ci gaban kuma, shugaban rukunin likitocin Sin dake aiki a kasar ta Nepal Lu Lin, ya bayyana cewa jami'an lafiyar sun kammala aikin bincike game da hadarin barkewar matsalolin lafiya da kan auku bayan bala'in girgizar kasa, kuma sakamakon ya nuna cewa za a iya samun yaduwar cututtuka bayan wannan mummunan bala'i.

Kafin hakan dai a ranar Juma'ar da ta gabata, rukunin ya tura masana tare da kayayyaki zuwa ofishin gwajin harkokin lafiya na kasar ta Nepal, domin bincikar wasu batutuwa 51 bisa manufar hukumar lafiya ta duniya WHO, ciki har da gwajin cutar mura, da atuni, da ingancin ruwan sha da sauransu. Aikin da ake sa ran zai taimaka wajen shawo kan barkewar cututtuka a yankunan da bala'in yafi shafa.

A nasa bangare, mataimakin shugaban tawagar likitancin na Sin Zhang Rong, ya bayyana damuwarsa kan yanayin da ake ciki, musamman game da batun shawo kan cututtuka masu yaduwa, inda ya bayyana cewa rukunin na Sin, na kokarin horar da rukunin 'yan kasar. Ya zuwa daren ranar Juma'a, an riga an horas da likitocin Nepal sama da 600, wadanda ake sa ran za su ziyarci wurare daban daban a cikin kasar, dauke da magunguna na shawo kan cututtuka, su kuma fadakar da al'umma dangane da hanyoyin magance barkewar cututtuka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China