Bisa labarin da aka bayar, an ce, bayan da aka kai kayayyakin agajin jin kai karo na farko da yawansu ya kai kudin Sin miliyan 20 ga kasar Nepal, bisa la'akari da halin da ake ciki a kasar, gwamnatin Sin ta yanke shawarar sake tura kayayyakin agaji karo na 2, don taimakawa Nepal farfadowa daga radadin girgizar kasa da ceton mutane. Kayayyakin agajin da za'a tura karo na 2 sun kunshi na'urorin tsabtace ruwa da kayayyakin jinya cikin gaggawa, da tantuna, da darduma, wadanda aka kiyasta darajarsu ta kai kudin Sin yuan miliyan 40.
A wannan rana, ayarin likitoci da Sin ta tura a Nepal, sun ci gaba da ceton mutane a yankunan da girgizar kasa ta rutsa da su. Tun daga safiyar ranar Litinin din makon nan da suka isa birnin Katmandu, hedkwatar kasar, nan take ne, suka fara gudanar da ayyukan ceton da ba da jinya, ya zuwa yanzu, an riga an ceci mutane kimanin 100.(Bako)