Wannan rukunin likitocin da ya fito daga lardin Sichuan na kasar Sin ya dauki na'urorin likitanci da kayayyakin yau da kullum, ana sa ran za a tabbatar da rukunin da zai gudanar da aiki da yin rayuwa har na makwanni biyu.
A yau 27 ga wata da karfe 10 na safe, tawaga ta farko ta rukunin ba da ceto na sojojin yankin Chengdu na kasar Sin dake kunshe da sojoji 55 ta tashi daga birnin Kunming na lardin Yunnan zuwa kasar Nepal don ba da ceto. Tawaga ta biyu dake kunshe da sojoji 45 za ta tashi daga kasar Sin a ranar 28 ga wata bisa shirin.
Sojojin 100 za su tafi Nepal tare da kare masu neman mutanen da suka bace 4, da motocin ceto 5 da na'urorin neman mutane da sauran na'urorin ba da ceto da dama. Bayan da suka iso kasar Nepal, za su fara gudanar da ayyukan neman mutane da ba da jinya da sauransu a dukkan fannoni. (Zainab)