in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nepal ya jinjinawa kwazon tawagar ceto ta kasar Sin
2015-05-02 17:11:07 cri
Shugaban kasar Nepal Ram Baran Yadav, ya bayyana wa wakilan kafofin watsa labaran kasar Sin irin godiyar da kasar sa ke yi, ga taimakon da gwamnati, da jama'ar kasar Sin suka baiwa yankunan kasar sa, da bala'in girgizar kasa ya aukawa a 'yan kwanakin baya. Shugaba Yadav ya kuma jinjinawa tawagar ceto ta kasar Sin game da managarcin aiki da ta gudanar a kasar ta Nepal.

Yadav ya kara da cewa, bayan aukuwar girgizar kasar, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da kuma firaministan kasar Li Keqiang, na cikin na sahun gaba wajen gabatar da sakon alhini ga kasar sa. Kana a yanzu haka da kasar ta Nepal ke fuskantar babbar barazana, ciki hadda mawuyacin halin rayuwa a duk fadin kasar, da karancin kayayyakin agaji, gwamnati da jama'ar kasar Sin na aikewa da ma'aikatan ceto, da na kiwon lafiya, da kuma kayayyakin agaji na gaggawa da al'ummar kasar.

Bugu da kari, tawagogin ceto, da na kiwon lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasar ta Nepal sun gaggauta isa yankunan dake cikin mawuyacin hali, inda suke gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, lamarin da ya sa kasar ta Nepal ke fatan Sin, za ta ci gaba da ba da wannan taimako, musamman a fannonin kandagarkin barkewar cututuka masu alaka da bala'in girgizar kasar. Baya ga batun taimaka wa jama'ar kasar wajen sake ginin kasa.

Kaza lika, shugaban kasar ta Nepal ya ce taimakon da Sin ta samar a lokacin da aka fi bukatar sa, ya shaida kasancewar ta abokiyar arziki ga Nepal, don haka Nepal din ke fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwar gudanar da aiki ceto, domin warware matsalar da ake fuskanta cikin gaggawa.

Rahotanni daga ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Nepal dai sun nuna cewa ya zuwa Asabar din nan, girgizar kasa da ta aukawa kasar, ta riga ta haddasa rasuwar mutane 6,659, yayin da wasu 14,062 suka jikkata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China