Ya ce, tawagar aiki ceto ta kasar Sin mai mutane 62 ta riga ta isa babban birnin kasar Nepal, Katmandu a ran 26 ga wata da rana, kuma tawagar ta fara aikin ceto da isar ta birnin ba tare da bata lokaci ba, Daga bisani kuma, tawagar likitoci mai kunshi da mutane 17 ta fara aikin ba da agaji a wurin.
Bugu da kari, karin tawagogin aikin ceto da likitoci dake kunshe da mutane 170 za su tashi zuwa birnin Katmandu domin shiga ayyukan ceto da kuma ba da agaji.
Kaza lika, jiragen sama guda hudu dake dauke da kayayyayin agaji na gaggawa da kasar Sin ta samar wa kasar Nepal za su isa kasar Nepal bi da bi a yau Litinin da kuma gobe Talata, kayayyakin sun hada da tantuna, barguna da dai sauransu, wadanda gaba daya suka kai ton 186.
Bugu da kari, wasu larduna, birane da al'ummar Sin suna kokarin samar wa kasar Nepal taimako cikin himma da kwazo. (Maryam)