in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na shirya kai wani sabon taimakon agaji ga Nepal
2015-05-04 14:58:31 cri
Shugaban tawagar samar da taimako ga kasar Nepal kan harkokin kiwon lafiya ta kasar Sin Xv Shuqiang ya bayyana a jiya Lahadi cewa, gwamnatin kasar Sin za ta fara shirin samar da wani taimakon agaji ga kasar Nepal, kuma a halin yanzu, ana tsara yadda shirin zai gudana.

Xv Shuqiang ya ce, za a samar da wani sabon taimako bisa bukatun kasar Nepal da kuma fasahohin kasar Sin game da yadda za a iya fuskantar bala'in girgizar kasa.

Rahotanni na cewa, a halin yanzu akwai tawagogin ba da jinya na kasar Sin dake gudanar da ayyukan ceto a kasar Nepal, Xv Shuqiang ya nuna godiya ga kokarin da tawagogin suka yi a kasar Nepal, kuma yana fatan za su ci gaba da samar da taimakon ba da agaji da kandagarkin barkewar cututuka masu alaka da bala'in girgizar kasar yadda ya kamata a kasar Nepal.

A wani ci gaba kuma, bisa gayyatar da gwamnatin kasar Nepal ta yi wa kasar Sin, da karfe 11 na safiyar yau Litinin 4 ga wata, wata tawagar kiwon lafiya mai kunshe da ma'aikata guda 30 da suka fito daga hukumar kiwon lafiyan yankin Tibet mai cin gashin kansa da kuma cibiyar yin rigakafi da hana yaduwar cututuka na yankin sun riga sun isa kasar Nepal, domin fara aikin kula da lafiyar jama'a da kandagarkin barkewar cututuka masu alaka da bala'in girgizar kasar a Nepal. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China