A jiya ne Valerie Amos, mataimakiyar babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai ta isa kasar Nepal domin tantance irin barnar da girgizar kasa ta haddasa kamar yadda mataimakin kakakin babban sakataren MDD Farhan Haq ya bayyana .
Haka kuma wasu hukumomin MDD suna nan suna rarraba kayayyakin rage radadin bala'i a kasar ta Nepal, tare da ba da tallafin kiwon lafiya.
Mista Haq ya bayyana cewa, madam Amos ta isa birnin Katmandu, hedkwatar kasar Nepal, sannan tana shirin ziyartar sauran wuraren da bala'in ya shafa. Sai ta bayyana cewa, ana fuskantar babban kalubale wajen rage radadin bala'in. Yanzu wasu jami'an hukumar kungiyar tarayyar Turai da hukumar samar da abinci ta duniya suna taimakawa wajen yaki da bala'in.
Haka zalika kuma, a cewar ofishin daidaita harkokin jin kai na MDD, ya zuwa yanzu ba a iya isa wasu yankunan karkara wadanda bala'in ya rutsa da su ba. Manyan matsalolin da ake fuskanta yanzu su ne rashin jiragen sama masu saukar ungulu, matsalar sadarwa ta waya ko wayar salula, da kuma matsalar tsaro da dai sauransu.
Ofishin ya kuma ruwaito adadin kididdiga da gwamnatin Nepal ta bayar na cewa, ya zuwa yanzu mutane kusan 5600 sun rasa rayukansu sakamakon mummunar girgizar kasar da ta abku a Nepal a ranar 25 ga watan Afrilu, yayin da wasu fiye da dubu 11 suka jikkata. (Tasallah Yuan)