A yau Talata ne da misalin karfe 11 na safe agogon Nepal jirgin saman sojan kasar Sin da ke dauke da kayayyakin rage radin bala'i da yawansu ya kai ton 186 ya sauka a birnin Katmandu, hedkwatar kasar Nepal
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin.Mista Hong ya fadi hakan yau a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing. Ya kara da cewa, wadannan kayayyaki sun kasance rukuni na farko ne. A sa'i daya kuma, tun a daren jiya Litinin sojoji masu aikin ceto da ma'aikatan kiwon lafiya 170 suka fara ayyukansu a wuraren da girgizar kasar ta shafa yayin da sauran ma'aikatan agaji 45 kuma za su tashi zuwa Nepal a yau Talata. (Tasallah Yuan)