Tuni dai wannan girgizar kasa biyu ta haddasa rasuwar mutane 2152, yayin da wasu mutanen kimanin dubu biyar suka jikkata.
Wani jami'i mai kula da harkokin soja a kasar ta Nepal ya bayyana cewa, ana ci gaba da aikin ceto, kuma mai yiwuwa ne adadin wadanda suka rasu sakamakon girgizar kasa ya yi matukar karuwa.
Bayan aukuwar wannan girgizar kasa guda biyu a kasar ta Nepal, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kira taron gaggawa a Lahadin nan, domin tattaunawa game da ayyukan ba da agaji ga kasar ta Nepal.
Haka kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga waya ga shugaban kasar Nepal, inda ya jaddada kudurin jama'ar kasar Sin na goyon baya, da taimakawa jama'ar kasar ta Nepal. Sa'an nan kuma, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya zanta da takwaransa na kasar ta Nepal ta wayar tarho, inda ya shaida masa aniyar kasar Sin, game da samar da taimakon gaggawa ga kasar ta Nepal.
Bugu da kari, bisa gayyatar da gwamnatin kasar Nepal ta yi wa kasar Sin, tawagar aikin ceto ta kasar Sin ta riga ta isa birnin Katmandu da safiyar Lahadin na, inda ba da bata lokaci ba ta fara gudanar da aikin ceto. A daya hannun kuma ana sa ran isar tawagar kiwon lafiya ta kasar Sin ta gaggawa zuwa Nepal a daren wannan rana ta Lahadi. (Maryam)