A ranar Lahadin nan ne ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Nepal, ta sanar da cewa mummunar girgizar kasar da ta auku a jiya Asabar, ta haddasa mutuwar mutane fiye da dubu 1 da dari 9, yayin da kuma wasu kusan dubu 5 suka jikkata, baya ga mummunar barna da annobar ta haddasa.
Rahotannin sun nuna cewa shugaba Xi Jinping na kasar Sin, da firaministan kasar Li Keqiang, sun aike da sakwannin jaje ga takwarorinsu na kasar ta Nepal. Kana ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta kaddamar da shirin gaggawa na ba da agajin jin kai, inda take hadin gwiwa da sauran hukumomi, a kokarin fito da shirye-shirye, tare da gudanar da ayyukan share fage ba da tallafi.
Tuni dai kungiyar ba da agaji ta kasar Sin mai kunshe da mambobi 62 ta isa filin jirgin saman birnin Kathmandu, fadar mulkin kasar ta Nepal, tare da wasu kayayyaki, da na'urorin ba da agajin da jinya.
A wani ci gaban kuma, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayyana juyayinsa ga gwamnatin Nepal, da al'ummar kasar wadanda girgizar kasar ta rutsa da su. Ya ce MDD za ta tallafawa gwamnatin Nepal, tare da daidaita ayyukan agaji na kasa da kasa, kana ta shirya gudanar da manyan ayyukan ceto a kasar.
Har wa yau kuma, kasashen duniya da dama na ci gaba da bayyana fatansu na baiwa Nepal taimako. Inda kasashen Rasha, da Singapore suka riga suka aike da tawagogin bada agaji. Kaza lika kungiyar bada agaji ta Red Cross, ta fara ayyukan bada agajin gaggawa a wuraren da bala'in ya shafa, tare da yin kira da samar da karin tallafin kudade.
A daya hannun kuma an fara gudanar da ayyukan rage tasirin wannan bala'i a jihar Tibet ta nan kasar Sin, sakamakon mummunar girgizar kasar da ta auku a kasar ta Nepal. (Tasallah Yuan)