A daya hannun kuma wani jami'in kasar India ya bayyana cewa mutane 14 sun hallaka, yayin da wasu sama da 10 suka jikkata a wani wurin dake gabashin India da kan iyakar kasar ta Nepal. Haka kuma ofishin jakadancin kasar Sin dake Nepal ya tabbatar da cewa, Sinawa 2 dake aiki a tashar Geelong dake iyakar Sin da Nepal sun rasa rayukansu sakamakon aukuwar bala'in.
Dadin dadawa, girgizar kasar ta yi tasiri matuka ga wasu yankunan dake jihar Tibet ta nan Sin. An kuma tabbatar da cewa mutane 7 sun mutu a gundumar Nyalam ta Sin, yayin da ake kuma ci gaba da tasirin girgizar kasar a yankin.
Bayan abkuwar wannan bala'i, wasu gine-gine a kasar ta Nepal sun lalace, yayin da girgizar kasar ta barnata turakun sadarwar wayar tarho. An kuma rufe filin jirgin saman Kathmandu na kasar Nepal.
Kaza lika an sauya hanyar da jiragen saman dake sauka a Kathmandu ke bi ya zuwa filayen jiragen sama na India. Ministan sadarwa na kasar ta Nepal ya yi kira ga kasashen duniya da su baiwa kasar sa taimakon gaggawa, domin shawo kan wannan annoba mai karfi.
Bugu da kari rahotanni na nuna cewa sakamakon abkuwar bala'in, an samu zaftarewar dusar kankara a kudancin babban dutsen Qomolangma. Girgizar kasar ta kuma yi tasiri matuka ga wurare da yawa dake gabas, da kuma arewacin India. Wani jami'in yankin uttar na India ya bayyana cewa, gine gine da yawa sun lalace a sakamakon hakan. An kuma dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa na karkashin kasa a birnin New Delhin kasar India na dan lokaci.
Baya ga Indiya da Sin, an ji tasirin wannan girgizar kasa a kasashen Pakistan, da Malaysia, da Bangladesh da sauransu.
Bayan aukuwar girgizar kasar, hukuma mai kula da girgizar kasa ta nan Sin ta dauki matakin tinkarar girgizar kasar. Inda hukumar ta jihar Tibet mai cin gashin kanta, ta tura wani rukunin ma'aikatan samar da agaji zuwa yankin da tasirin girgizar kasar ya shafa, domin gudanar da aikin sa ido, da yin bincike da ma sauran matakai. Hukumomin sufuri da rundunar soja sun tura mutane da motoci zuwa yankin da ke fama da bala'in domin yin gyare-gyare ga hanyoyin dake wurin.
Yanzu kungiyoyin aikin ceto na duniya 29 suna mai da hankali kan bala'in bisa tashar yanar gizo ta MDD, ciki har da kungiyar ta Sin wadda a shirye take ta samar da agaji a ko da yaushe.(Fatima)