in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan littafin da shugaban Sin ya rubuta da aka sayar ya kai sama da miliyan 4
2015-04-15 16:52:35 cri

Mataimakin shugaban kamfanin wallafa litattafai na kasar Sin Lu Cairong ya sanar a wani bikin baje kolin litattafai da aka yi a birnin London a ran 14 ga wata cewa, yawan littafin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta mai suna "Tunanin Xi Jinping kan harkokin daidaita ayyukan kasa" da aka sayar ya kai fiye da miliyian 4, daga cikinsu, an sayar da kimanin dubu 400 a ketare, abin da ya kai matsayin farko na wallafa litattafan da shugabannin kasar Sin suka rubuta a ketare tun bayan shekarar 1978.

Wannan littafin da Mr Xi ya rubuta, an fassara shi zuwa harsuna da dama, tun lokacin da aka gabatar da shi a bikin baje kolin litattafai na Frankfurt a kasar Jamus a watan Oktoba na shekarar 2014, al'ummar duniya na zura ido sosai kan wannan littafi. Shugabannin kasashe daban-daban da wasu tsoffin shugabanni da wasu shahararrun masana kan batun kasar Sin sun darajanta littafin sosai, kuma wasu manyan kafofin yada labaru na kasashen yamma sun ba da labarai kan wannan littafi fiye da 400, don ba da bayani da sharhi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China