in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da ministar harkokin wajen Indiya
2015-02-02 20:41:05 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da ministar harkokin wajen kasar Indiya madam Sushma Swaraj a nan Beijing, fadar mulkin kasar Sin a yau Litinin 2 ga wata.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya jaddada cewa, wajibi ne kasashen Sin da Indiya su yi hakuri wajen daidaita sabanin da ke tsakaninsu, a kokarin ganin sabanin bai kawo illa ga huldar da ke tsakaninsu ba. Sa'an nan ya kamata su nuna sahihanci wajen kara azama kan warware batutuwan da abin ya shafa yadda ya kamata.

Yace Kasar Sin na son inganta tuntubar juna da taimakawa juna da kasar Indiya a fannin tafiyar da harkokin kasa da kasa da sauran muhimman al'amura a kokarin sa kaimi kan kara raya duniya cikin adalci, da kiyaye moriyar kasashe masu saurin bunkasa ta fuskar tattalin arziki da kasashe masu tasowa. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China