A cikin wata sanarwa, ministan ya bayyana cewa taron zai kasance da wata manufar bullo da hanyoyin warware matsalolin dake da nasaba da ta'addanci da kuma samar da wasu dabarun Afrika wajen yaki da wannan barazana.
A kalla shugabannin kasashe da gwamnatoci goma ne ake sa ran za su halarci wannan zaman taro, in ji sanarwar da ta zo a lokacin da barazanar mayakan kungiyar Al-Chebaab ta Somaliya ta zama wani babban kalubale ga kasar Kenya.
Kwararru a fannin tsaro na ganin cewa laifuffukan kasa da kasa da sumogal din muyagun kwayoyi na kawo sauyi ga ci gaban siyasa, jama'a da tattalin arzikin nahiyar Afrika a halin yanzu kana suna taimakawa ta'addanci.
AU ta gabatar da wani shirin kafa wani karamin kwamiti na mambobi biyar na kwamitin yaki da ta'addanci da sumogal hodar ibilis bisa tsarin yin bincike a kai a kai kan makomar ta'addanci da hana samun kudade ga kungiyoyin ta'addanci. (Maman Ada)