Shugaban kungiyar AU a wannan karo, kana shugaban Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz Mohamed Ould Abdoul Aziz a cikin jawabinsa na rufe taron ya bayyana cewa, a yayin taron kuma, wakilai mahalarta taron sun yi shawarwari kan shirin bunkasa aikin noma a nahiyar Afirka a nan gaba, da kuma yanke shawarar kara saurin canza hanyar bunkasa aikin noma, da sa kaimi ga zamanintar da aikin noma na Afirka, da ci gaba da aiwatar da shirin bunkasa sha'anin noma na Afirka da sanarwar Maputo, da kara samar da manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da sa kaimi ga samun dauwamammen ci gaba, da kawar da talauci da karancin abinci bisa iyakacin kokari.
An bude wannan taro ne a ranar 26 ga wata, bisa taken "Tsaron aikin noma da samar da isashen abinci". A yayin taron, shugabanni da wakilai daga kasashe sama da 50 na kungiyar AU sun yi shawarwari kan yin kwaskwarima ga aikin noma, da sanya babban burin Afirka na shekarar 2063, da sauransu. Bayan haka, an mai da hankali sosai kan yanayin da ake ciki a fannin tsaro da aikin jin kai a kasar Afirka ta Tsakiya, Kongo Kinshasa, Sudan ta Kudu da dai sauransu. (Fatima)