An dai bude zaman ne a jiya Juma'a, a hedkwatar kungiyar AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha, gabanin babban taron AU karo na 24 dake tafe a karshen watan nan na Janairu.
Wakilai daga kasashen nahiyar Afirka sun tattauna game da batun aiwatar da shirin bunkasa harkokin mata, da ake shirin kaddamarwa a wannan shekara, shirin da ke kunshe da manufofin inganta rayuwar 'ya'ya mata daga bana zuwa shekarar 2063.
Cikin jawabin da ya gabatar, mataimakin shugabar kwamitin gudanarwar kungiyar ta AU Erastus Mwencha, ya ce lokaci ya yi, da kasashen Afirka za su hada gwiwa, su fuskanci alkibla daya, domin dora nahiyar kan turbar hadin kai da samun ci gaba, matakin da zai baiwa nahiyar damar samun daukaka mai dorewa cikin yanayin zaman lafiya da lumana.