Takardun mika taimakon an rattaba hannu kansu tsakanin ministan tsaron kasar Mali da jami'in dake kula da harkokin ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Mali, Guo Xueli.
A cewar mista Guo Xueli, samar da wadannan taimako, na bisa tsarin yarjejeniyoyin bada tallafin kayayyakin soja da kasashen biyu suka sanya wa hannu a cikin watan Maris da Augusta na shekarar 2013, dake da manufar taimakawa sojojin Mali gudanar da ayyukansu na tsaron kasa yadda ya kamata.
Da yake barkar wannan taimako wanda ya kara bisa wani taimakon kayayyakin sadarwa da aka bada tun a shekarar 2013, da darajarsu baki daya ta kai ga RMB yuan miliyan 20 (kimanin kudin Sefa biliyan 1,6), ministan tsaron kasar Mali ya nuna yabo ga kasar Sin, kasar da ko da yaushe take tallafawa kasar Mali da jami'an tsaronta, ta hanyar baiwa sojojinta fasaha da kwarewa a fannin isar da bayanai da sadarwa da kuma karfafa musu karfin gudanar da ayyukansu.
Ministan tsaron kasar Mali ya kuma yi maraba da zuwa wani rukunin sojojin zaman lafiya na kasar Sin a cikin tawagar MDD dake kasar Mali (MINUSMA) da kuma jinjinawa huldar dangantakar soja dake kara yaukaka a lokacin baya bayan nan ta hanyar samar da taimako da dama da kuma yadda kasar Sin ke sanya hannun a wasu muhimman fannoni na rayuwar al'ummar kasar Mali, kamar misalin gine-gine, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da masana'antu. (Maman Ada)