Ofishin tawagar MDD mai kula da cutar Ebola dake kasar Mali ya bayar da sanarwa cewa, bisa ma'aunin hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, idan ba a gano sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a cikin kwanaki 42 a jere ba, ana iya sanar da cewa,an kawo karshen cutar a kasar. Wannan na cewa, yanzu kasar Mali ta kawar da cutar Ebola a kasar.
Bisa kididdigar da hukumar WHO ta yi, an ce, tun lokacin da cutar Ebola ta bulla a shekarar bara, mutane 21296 suka kamu da cutar, yayin da kuma mutane 8429 suka mutu a sakamakon cutar. Yayin da yawan mutanen da suka mutu a sakamakon cutar a kasar Mali ya kai 7. (Zainab)