in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mutane 3 sun rasu yayin wata tarzoma a sansanin MINUSMA
2015-01-28 16:15:06 cri
Mutane uku sun rasu sakamakon wata zanga-zanga da ta auku a sansanin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Mali.

Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga-zanga kimanin 1000 ne suka gudanar da gangami a sansanin tawagar ta MINUSMA dake birnin Gao, a arewacin kasar ta Mali a ranar Talata 27 ga wata, lamarin da ya sanya dakarun MINUSMA amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

An ce wasu daga masu zanga-zangar sun kutsa kai cikin sansanin na MINUSMA, an kuma ji karar yin harbi da bindiga a cikin sansanin. Sai dai kakakin MINUSMA Olivier Salgado, ya bayyanawa taron manema labaru da aka gudanar a birnin Bamako cewa, tawagar ta yi amfani da barkonon tsohuwa ne kadai wajen tarwatsa masu zanga-zanga a kofar sansanin.

Ya ce an harba bindiga ne domin kashedi ga wasu da suka yi yunkurin shiga sansanin. Koda yake bai bayyana ko jami'an tsaron tawagar sun harbi masu zanga-zanga ko a'a ba.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, dakaru masu goyon bayan gwamnatin kasar Mali dake arewacin kasar ne suka nuna rashin jin dadi, ga manufar tawagar MINUSMA ta haka su gudanar da zanga-zanga. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China