Kwamitin sulhun MDD ya nuna rashin jin dadi ga ci gaba da barkewar tashe-tashen hankula a arewacin kasar, lamarin dake haddasa rasa rayuka, tare da jikkatar fararen hula. Don gane da hakan ne kwamitin ya bukaci bangarori daban daban, dasu dakatar da ayyukan nuna karfin tuwa, tare da rungumar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka daddale a bara.
Ban da wannan, kwamitin sulhu ya ce zai nazarci bukatar kakaba takunkumi ga wadanda ke da hannu cikin daukar matakan nuna karfi, da masu keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Malin.
Kawo yanzu dai ana ci gaba da fama da tashe-tashen hankalu a arewacin Kasar ta Mali. Koda yake kasar Algeria, da MDD, da sauran masu ruwa da tsaki na ci gaba da shiga tsakani, inda ake fatan farfado da shawarwari tsakanin bangarorin kasar biyu a ranar 8 ga watan nan a birnin Algiers.(Fatima)