Rahotanni sun ce jami'an tawagar 7 sun samu raunuka, bayan da wani Bam ya tashi da motar da suke ciki a jiya Juma'a, a wani wuri dake kusa da filin jirgin saman Kidal.
Tuni dai aka garzaya da wadanda harin ya rutsa da su zuwa asibiti, ya yin da jami'an tsaro ke ci gaba da bincike a wurin da Bam din ya tashi.
A daya hannun kuma tawagar ta MINUSMA ta yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki, da su martaba kudurin da aka cimma cikin watan Satumba a birnin Algiers, wanda ya tanaji dakatar da kaiwa jami'an wanzar da zaman lafiya hare-hare.
Harin dai na wannan karo shi ne na baya bayan nan da aka kaiwa jami'an na MNUSMA, tun bayan makamancinsa, da aka kaiwa jami'an a Gao dake Arewacin kasar a ranar Lahadin makon jiya, wanda shi ma ya raunata jami'an na MINUSMA su 8.
Arewacin Mali dai ya zamo matattarar 'yan tawayen kasar, tun bayan juyin mulkin kasar na watan Maris a shekara ta 2012.