Wasu mutane biyu da suka kamu da cutar Ebola mai tsanani sun warke sarai, bayan da suka samu kulawa a asibitin sada zumunci na Sin da Saliyo dake birnin Freetown fadar mulkin kasar Saliyo.
Rahotanni sun bayyana cewa a safiyar ranar 4 ga wata, wadannan mata biyu sun bar asibiti, kuma su ne na farko da suka warke bisa ga tallafin jiyya da suka samu daga wajen rukuni na hudu na tawagar likitocin da kasar Sin ta tura zuwa Saliyo .
Masu aikin jiyya na Saliyo da na Sin sun kwashe kwanaki 20 suna iyakacin kokarin su wajen baiwa marasa lafiyar taimako, kafin daga bisani aka tabbatar sun samu lafiya bayan an yi musu gwaji har sau biyu. Matakin da ya karawa masu aikin jiyya Sinawa kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu. (Amina)