in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Saliyo ya yaba da muhimmin taimakon Sin wajen yaki da Ebola
2015-03-12 10:54:13 cri

Wani babban jami'in kiwon lafiya na kasar Saliyo ya nuna yabo ga muhimmin kokarin da kasar Sin ta bayar wajen yaki da cutar Ebola a nahiyar Afrika, inda ya bayyana cewa, babu wasu sharudan da aka gindiya game da taimakon kasar Sin.

Dokta Brima Kargbo, babban likita a ma'aikatar kiwon lafiya, ya jinjinawa muhimmin taimakon jin kai na kasar Sin zuwa ga Saliyo tun farkon barkewar wannan cuta da ta halaka a kalla mutane dubu goma. Mista Kargbo ya bayyana cewa, kwararrun likitoci da kayayyakin kasar Sin sun taimaka sosai wajen kawar da munanan illolin annobar Ebola. Kasar Sin ta gudanar da babban shirinta na ba da taimako ga kasashen waje a fannin kiwon lafiya tun lokacin barkewar annobar Ebola ta hanyar kawo taimakon jin kai da darajarsa ta kai fiye da dalar Amurka miliyan 120, tare da kuma tura daruruwan likitoci a yankunan da ake fama da cutar a Afrika.

Haka kuma kasar Sin ta zuba fiye da dalar Amurka miliyan goma ga kungiyoyin kasa da kasa bisa tsarin kokarin hadin gwiwa na kawar da wannan cuta mai kisa.

Dokta Kargob ya tunatar da cewa, a yayin da annobar ke kamari a kasar a cikin watan Mayun da ya gabata, jakadan kasar Sin dake Saliyo, Zhao Yanbo, ya yi wa kasar alkawarin kafa dakin binciken cututtuka mai inganci, da aka karba a cikin watan Nuwamban da ya gabata. Yanzu aiki ya kammala da hada kayayyaki, kuma a shirye don gudanar da bincike na duk wasu na'o'in cututtuka masu lalata jiki, da ma cututtuka masu yaduwa, in ji mista Kargob.

A cewarsa, dakin binciken zai taimaka a matsayin cibiya ta farko domin sanya ido kan cututtuka a Saliyo, da ma shiyyar yammacin Afrika baki daya. Game da abin da zai biyo bayan Ebola, dokta Kargob ya bukaci taimakon Sin, musammun ma wajen gina tsarin kiwon lafiya na Saliyo. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China