Ganin cewa shirin "babu mutum daya mai dauke da cutar Ebola a cikin kwanaki 60" da ya kawo karshensa a ranar 10 ga watan Maris, bai samar da sakamakon mai kyau ba, kwamitin yaki da cutar Ebola na kasar Guinea ba zai yi kasa da gwiwa ba a cikin yakin da yake da wannan cuta, yanzu yana mai da hankali kan wani shirin yaki da wannan annoba da zai kai har zuwa ranar 15 ga watan Afrilu.
A cewar Fode Tass Sylla, mai kula da hulda da jama'a cikin wannan kwamitin, wannan shirin na da manufar karfafa karfin tawagogin ma'aikatan kiwon lafiya na kwimitin dake gudanar da aiki a Conakry, babban birnin kasar, da garuruwan dake kewaye da suka hada da Coyah, Dubreka, Boffa, Kindia da Forecariah.
Mista Sylla ya yarda cewa, burin kwamitin yaki da cutar Ebola da kuma abokan huldarsa a fannin kiwon lafiya, da suka da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO), kungiyar likitocin kasa da kasa da cibiyar shawo kan cututtukan Atlanta, sun yi dogaro ne da shirin "babu mutum daya mai dauke da Ebola a cikin kwanaki 60" bai cimma nasara ba.
Dalilan da suka hadasa rashin nasara su ne dari darin da mutane suke nunawa, da kuma labarai maras tushe da ake yadawa. Kalubale biyu da kwamitin ke dauka a matsayin wadanda suka mai da hannun agogo baya ga aikinsu, da kuma suka gurgunta kokarin da aka yi, musammun ma a yankin Basse Guinea, da birnin Conakry, da kuma yankunan Boffa, Forecariah, Kindia, Coyah da Dubreka. (Maman Ada)