A kasar Guinea, an gudanar da bikin ranar mata ta duniya a ranar 8 ga watan Maris, a karkashin jagorancin hukumomin kasar da kungiyoyin ba da tallafin ci gaba, bisa taken yaki da cutar Ebola, in ji wakilin Xinhua. Idan taken "Yancin mata, 'yancin bil'adama" ya kasance taken da MDD ta gabatar, amma a kasar Guinea, taken ya canja zuwa "Mata a gaban Ebola", domin tunawa da yawan asarar matan da aka yi a lokacin rikicin kiwon lafiya dalilin cutar Ebola.
A karkashin jagorancin matar shugaban kasar, madam Conde Djene Kaba, bikin ya samu halartar manyan jami'ai da suka hada da faraminista Mohamed Siad Fofana da mambobin gwamnati, da kuma wakilan kungiyoyin ba da lamuni dake tallafawa kasar Guinea a cikin yakin da take da wannan cuta.
Ranar dai mata, ta kasance wata babbar dama ga gwamnatin Guinea da abokan hulda a fannin kiwon lafiya wajen bullo da dabaru da nagartattun ayyukan taimakawa matan da illolin annobar cutar Ebola suka shafa. Tun cikin watan Maris na shekarar 2014, a farkon barkewar cutar a kasar Guinea, fiye da kashi 55 cikin 100 na mutanen da cutar ta shafa mata ne, da shekarunsu ke tsakanin 15 da 40. (Maman Ada)