Bisa kididdigar da ofishin yawon shakatawa na MDD wato UNWTO ya yi, ya nuna cewa, adadin masu yawon shakatawa a nahiyar Afirka ya karu da kashi biyu bisa dari a shekarar 2014, idan aka kwatanta da na shekarar 2013, amma adadin ya ragu sosai idan aka kwatanta da na nahiyoyin Turai, Asiya ko Amurka. Kafin shekarar 2014, adadin karuwar masu yawon shakatawa a Afirka a ko wace shekara ya kan kai kashi 4.8 bisa dari, amma adadin ya ragu sabo da yaduwar cutar Ebola a nahiyar.
Haka kuma, bayan da aka kawo karshen yakin basasa a kasar Saliyo a shekarar 2000, adadin karuwar masu yawon shakatawa a kasar ya kai kashi 10 bisa dari a ko wace shekara, amma adadin masu yawon shakatawa a kasar ya ragu da kashi 46 bisa dari a shekarar 2014 bisa kididdigar da UNWTO ya yi.
Babban sakataren UNWTO Taleb Rifai ya bayyana a yayin taron baje kolin yawon shakatawa na Berlin na kasar Jamus cewa, duk da cewa, cutar Ebola ta shafi manyan kasashe guda uku, amma kalubalan da cutar ta haddasa ga sana'ar yawon shakatawa ya shafi dukkan fadin nahiyar Afirka, inda masu yawon shakatawa da dama ba su son zuwa yawon shakatawa a Afirka sabo da tsoron cutar. (Maryam)