Mr. Nyenswah ya ce yanzu haka an kwashe kwanaki 18, tun bayan samun mutum na karshe da ya kamu da cutar a gundumar Montserrado, gundumar da a baya ta kasance wurin da aka fi samun yaduwar cutar.
Ya ce wasu gundumomin kasar sun kai makwanni 3 ko fiye, ba tare da samun sabbin masu kamuwa da Ebola ba.
Duk da wannan nasara da ake ci gaba da samu a sassan kasar, mai magana da yawun shirin yaki da cutar na MDD a Laberian Lisa white, ta ja hankalin al'ummar kasar da su yi taka-tsantsan, kasancewar iyakokin Laberia da kasashen dake ci gaba da yaki da cutar na bude a yanzu haka.