Kasar Liberiya ta sallami maras lafiya na karshe da ya kamu da cutar Ebola daga wata cibiyar kasar Sin dake kula da masu fama da cutar Ebola (ETU).
A halin yanzu babu mutum guda har zuwa wannan rana da aka tabbatar ya kamu da Ebola a cikin cibiyoyin jinya 19 na ETU dake Liberiya. A yayin wani gajeren bikin da aka shirya a Monrovia, shugaban ETU na kasar Sin, kanal Yang Haiwei, ya bayyana cewa, maras lafiya guda da aka tura asibiti a ranar 18 ga watan Febrairun shekarar 2014 yana cikin hali mai tsanani a lokacin. Amma bayan kwanaki 15 da samun jinya daga tawagar likitancin kasar Sin, a karshe wannan maras lafiya ya samu sauki, in ji mista Yang, tare da bayyana cewa, yana daga cikin mutanen da aka ceto rayukansu a cibiyar ETU ta kasar Sin. Amma kuma duk da haka ya yi kashedi kan illolin da za su biyo baya idan har ba'a girmama matakan da suka shafi Ebola ba a wuraren da ake fama da cutar a kasar.
Wannan nasara da aka samu za ta iyar kasancewa ta 'dan lokaci, amma duk da haka wani muhimmin mataki ne. Tawagar likitancin kasar Sin za ta ci gaba da ba da nata kokari domin yaki da cutar Ebola, in ji mista Yang. (Maman Ada)