Shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma ya bada umurni a ranar Asabar ta hanyar kafofin rediyo da talabajin na kasar ga al'ummar kasar baki daya dasu tsaya gidajensu a tsawon wannan lokaci, a matsayin wata hanyar neman kawar da cutar Ebola kwata kwata daga wannan kasa.
Mista Koroma ya kuma bayyana cewa ranakun 4, 11 da 18 ga watan Afrilu a matsayin ranakun tsaya wa gida domin baiwa fararen hula damar sanya hannu cikin kokarin da ake na cimma burin ba bu mutum ko guda mai dauke da cutar Ebola.
A tsawon wannan lokaci na hana fita, ba za a gudanar da harkokin kasuwanci ba a dukkan fadin kasar. Sai dai ma'aikatan lafiya, masu aikin sa kai a yayin kamfen, jami'an tsaro da kuma manema labarai kadai ne zasu rika kaiwa da kawowa. (Maman Ada)