Kasar Liberiya ta gano wasu sabbin mutane biyu da ake zargin su da cutar Ebola, a yayin da kasar ta ba da sanarwa a ranar Jumma'a cewa, ta gano wani mutum guda mai wannan cuta, duk da cewa kuma kasar ta kwashe makwanni da dama ba ta samu cutar ba, in ji wani jami'in kasar.
Babban darektan tsarin kula da haduran Ebola, mista Francis Kateh ya bayyana cewa, daya daga cikin mutanen da suka kamu da cutar wata mata ce mai shekaru 44 da haifuwa wadda kuma aka tabbatar tana dauke da kwayoyin wannan cuta a asibitin wurin, yayin da mutum gudan da ake zargi ba shi da alaka da cutar Ebolan da aka gano baya bayan nan a wannan kasa, kuma a yanzu haka yana samun jinya a wani asibitin gwamnati. (Maman Ada)