Wakilan kasashen Saliyo, da Guinea da Liberia, sun gudanar da wani taro a birnin Freetown, fadar gwamnatin kasar Saliyo, domin tattauna batun sake ginin kasashen bayan shawo kan cutar Ebola.
Taron wanda ya samu halartar ministoci, da wakilan gwamnatocin kasashen 3, da na hukumomi, da kungiyoyin masu ruwa da tsaki, ya gudana ne bayan kammalar wani taron na yini biyu a birnin Conakry, wanda shugabannin kasashen 3 suka gudanar.
Da yake jawabi gaban mahalarta taron, ministan ma'aikatar kudin kasar Saliyo Dr. Kelfalla Marah, ya ce, za su yi amfani da wannan dama wajen nazartar kudurorin da shugabannin kasashen nasu suka cimma, game da karasa kakkabe cutar Ebola daga kasashen.
Ya ce, duk da nasarar da aka samu ta dakile yaduwar cutar, a hannu guda cutar ta bar mummunan tasiri a fannin tattalin arziki, da na zamantakewar al'umma, duba da irin asarar rayuka, da gurgunta harkokin lafiya da ta yi a kasashen 3. Baya ga hasarar haraji, sauran fannonin da cutar ta lahanta sun hada da fannin kamfanoni da masana'antu masu zaman kansu.
Daga nan sai ministan ya bayyana aniyarsu, ta nazartar tsare-tsaren sake ginin kasashen 3, gabanin taron da bankin duniya, da asusun IMF za su gudanar a birnin Washington a ranar 9 ga watan Afirilun dake tafe.
A daya hannun kuma za su nazarci tsare-tsaren da bankin raya Afirka na ADB ya tanada, game da samar da muhimman ababen more rayuwa a yankin da cutar ta fi ta'adi. (Saminu)