Babban magatakardan MDD Mr Ban Ki Moon ta bakin kakakinsa, ya ba da wata sanarwa a ran 4 ga wata, inda ya bayyana takaicinsa kan rashin kira wani taron share fagen shawarwari tsakanin sassa daban daban na kasar Sudan.
Kazalika, Mr. Ban ya kalubalanci bangarorin daban-daban a Sudan da su nuna himma da kwazo don shiga shawarwari tun da wuri, a sa'i daya kuma ya yabawa kokarin da rukuni na musamman mai kula da harkokin Sudan na AU ke yi ta fuskar warware rikicin kasar, kuma ya nanata cewa, majalisar za ta ci gaba da samar da tallafi a wannan fanni.
An ba da labari cewa, rukunin ya sanar a kwanan baya cewa, an dage taron share fagen shawarwari tsakanin sassan Sudan da aka shirya kiran shi a birnin Addis Ababa hedkwatar kasar Habasha a wannan makon da muke ciki, bisa dalili cewa, jam'iyyar dake rike da shugabancin kasar wato NPC da abokan kawancenta sun ki halartar taron. (Amina)