A yayin ganawar tasu ta ranar Litinin, shugaba Elbashir ya bayyana cewa, Sudan da kasar Sin na da dadaddiyar zumunta da dangantaka mai karfi. Ya ce hadin gwiwar kasashen ya kasance misali na irin kyakkyawar alakar dake akwai tsakanin kasashe masu tasowa. Kana kasashen biyu sun fahimci juna, suna kuma goyon bayan juna kan batutuwan kasa da kasa da na yankuna.
Shugaba Albashir ya kara da cewa an cimma nasarar gudanar da shawarwari karkashin kungiyar raya IGAD, game da shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu, wanda kasar Sin ta yi kira da a gudanar. Kuma wadannan shawarwarin na taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga wanzuwar zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu. A halin yanzu kasashen biyu suna fuskantar damar kara raya dangantakarsu, kuma kasar Sudan na kokari tare da Sin, wajen kara harkokin hadin gwiwa a sabbin fannoni, da hada kai wajen tabbatar da tsaro a yankin, da kuma daga dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi.
A nasa bangare, Wang Yi ya bayyana cewa, Sin na dora muhimmanci kan zumuncin dake tsakaninta da kasar Sudan, kuma tana fatan kara inganta dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu a fannin manyan tsare-tsare cikin dogon lokaci. (Zainab)