in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi shawarwari tare da ministan harkokin wajen kasar Sudan
2015-01-12 16:34:09 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Sudan Ali Ahmed Karti a birnin Khartoum na kasar Sudan a ranar 11 ga wata da dare.

A yayin wannan ganawa, Wang Yi ya bayyana cewa, burin ziyararsa a kasar Sudan shi ne bayyana matsayin kasar Sin na dora muhimmanci ga dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sudan, da goyon bayan da Sin ta nunawa kasar Sudan wajen tabbatar da zaman lafiya, da kuma bayyana fatanta na kara yin hadin gwiwa tare da Sudan a yayin da gwamnatin Sudan take hobbasa wajen raya tattalin arziki. Haka kuma Wang Yi ya bayyana cewa, Sin ba ta canja manufar raya dangantaka a tsakaninta da Sudan ba, kuma za ta kara mai da hankali ga dangantakarsu a yayin da take aiwatar da manufofin raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka da kasashen Larabawa.

A nasa bangare, Karti ya bayyana cewa, Sudan ta nuna yabo da godiya ga kasar Sin domin ta bada gudummawa sosai yayin da Sudan take fuskantar mawuyacin hali, kuma tana son ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Sin kan manyan batutuwan dake shafar kasar Sin. Kana kasar Sudan tana fatan cigaba da fadada hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin a fannonin aikin gona, ma'adinai da sauransu, da kara tabbatar da tsaron jama'ar kasar Sin da kamfanonin kasar dake Sudan, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da Sin kan batun kiyaye zaman lafiya da tsaro a yankunan kasar Sudan, da kuma inganta dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China