A daren ranar Alhamis ne dai shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir, da tsohon mataimakinsa, kuma jagoran 'yan adawar kasar Riek Machar, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen musayar wuta.
Jagororin biyu sun kuma amince su gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu, tare da aiwatar da yarjejeniyar da ta kunshi batutuwa 43, ciki hadda gyaran kundin tsarin mulkin kasa, da batun rabon iko.
Sauran batutuwan da aka amince da su sun hada baiwa 'yan jam'iyyar 'yantar da kasar ikon kada kuri'a yayin zabukan kasar, da ma ikon shiga takara, tare da sulhuntawa da neman yafiyar jama'ar bisa abkuwar yakin basasar da ya daidaita kasar.
A watan Yulin shekarar 2013 ne dai shugaba Kiir ya sauke Riek Machar daga mukamin mataimakinsa. Matakin da ya haifar da babbar baraka, da bambancin ra'ayi tsakanin manyan rassan kasar biyu.
Kaza lika rashin jituwa tsakanin sashen gwamnati da na tsohon mataimakin shugaban kasar ya janyo aukuwar tashe-tashen hankula a sassa da dama na kasar. Matakin da ya haifar da asarar rayukan sama da mutum dubu 10 cikin shekara guda.(Fatima)