Cikin sanarwar da ofishinsa ya fitar a jiya Juma'a, Ban Ki-moon ya yi kira ga bangarorin biyu, da su kai zuciya nesa, su kuma kauracewa ci gaba da kaiwa juna farmaki.
Har wa yau Mr. Ban ya jaddada cewa, ci gaba da daukar matakan soja ba zai warware rikicin dake fuskantar kasar ba, don haka ya dace a ci gaba da gudanar da shawarwari ko a kai ga cimma warware takaddamar dake tsakanin kasashen biyu ta hanyar siyasa.
Bugu da kari, Mr. Ban ya yabawa kokarin da kungiyar bunkasa gabashin Afirka gaba ta IGAD ke yi, wajen tallafawa shirin warware rikicin kasar ta Sudan ta Kudu, yana mai cewa kwamitin sulhun MDDr ya tsaida kudurin kakaba takunkumi, ga wadanda ke yiwa shirin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudun kafar-ungulu, ciki hadda takunkumin hana fita kasashen waje, da kuma daskaras da kudade ko kadarorinsu.
Bisa shiga tsakanin da kungiyar ta IGAD ke yi, ya zuwa yanzu bangarorin biyu sun cimma wata yarjejeniya cikin watan Fabrairun da ya gabata, wadda ta kunshi shirin kammala shawarwari tsakaninsu, kafin ranar 5 ga watan Maris din nan, kana a fara gudanar da shirin mika mulki a ranar 1 ga watan Afrilun dake tafe, sai dai bangarorin biyu sun gaza kammala shawarwarin bisa wa'adin da aka tsara, kana sun sanar da dakatar da shawarwarin da suke gudanarwa a jiya Jumma'a 6 ga wata. (Maryam)