Wang Yi wanda ya yi wannan bayanin a kasar Sudan ranar Lahadi ya ce, a shekarun baya, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa warware matsalar Sudan bisa bukatun kasar Sudan, da daidaiton da kasa da kasa suka cimma, da kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya zartas.
Minista Wang Yi ya ce, Sin tana yi hadin gwiwa tare da Sudan da Sudan ta Kudu a fannin man fetur, abin da ke samar da moriya ga dukkaninsu. Amma idan yake-yake ko tashin hankalin da aka samu suka yi tasiri ga sha'anin samar da man fetur, da farko za a kawo illa ga jama'ar Sudan da ta Sudan ta Kudu, babu shakka kasar Sin ba ta son gan irin wannan hali. Ya kuma tabbatar da cewa, kasar Sin ta yi shiga-tsakani kan matsala a tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu don daukar alhakin kanta kan harkokin kasa da kasa, ba don samun moriyarta ba. Don haka, a matsayinta na abokiyar Sudan da Sudan ta Kudu, Sin za ta ci gaba da yin kokari wajen daukar alhakinta. (Zainab)