UNICEF din ya yi bayanin cewa, da farko wadannan dakaru sun taru a wani matsuguni, daga baya suka ruga a guje cikin gidajen matsugunin inda suka tara yaran tare da yin garkuwa da yaran da yawancin su ba su wuce shekaru 12 da haihuwa ba.
Wakilin asusun na UNICEF a Sudan ta Kudu, Jonathan Fitch ya bayyana cewa, wannan danyen aiki ya keta dokokin kasa da kasa. Yin garkuwa da yara da sa su shiga rikicin dakaru, hakan zai lalata iyalai da zaman al'umma baki daya.
An fara rikici a kasar Sudan ta kudu tun daga watan Disamba na shekarar 2013, wadanda suka haddasa mutuwar mutane sama da dubu 10, yayin da wasu sama da miliyan daya suka rasa gidajensu.(Fatima)