Wannan dai shi ne karon farko da kasashe mambobin kumgiyar suka halarci bikin tun shekarar 2010 lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar Entebbe, wadda ta bukaci a raba ruwan kogin tsakanin kasashen. Koda ya ke kasar Masar ta ki amincewa da wannan yarjejeniya,inda ta kaurace wa taron,domin tana ganin yarjejeniyar na iya hana ta amfana da ruwa kamar yadda take bukata idan aka raba ruwan tsakanin kasashen kamar yadda yarjejeniyar ta bukata.
Masu fashin baki na ganin cewa, halartar bikin da Masar ta yi a wannan karo, ya kara ba da haske kan irin rawar da Sudan ta taka kan wannan batu.
Bikin kungiyar kasashen da kogin Nilu ya ratsa su shi ne bikin kungiyar na NBI mafi girma da ake gudanarwa a ranar 22 ga watan Fabrairun kowace shekara, tun lokacin da aka kirkiro kungiyar a shekarar 1999, da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen da kogin Nilu ya ratsa.
Kasashen kungiyar sun hada da Masar, Sudan, Sudan ta kudu, Uganda, Habasha, Jamhuriyar demokiradiyar Congo, Burundi, Tanzaniya, Rwanda, Kenya da kuma Eritrea.
Taken bikin na bana shi ne ruwa da inganta rayuwar jama'a