Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta jaddada a ranar Asabar niyyarta ta sanya takunkumi ga bangarorin dake yaki da juna a kasar Sudan ta Kudu.
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, takunkumin zai shafi wadanda ke ci gaba da yin zagon kasa ga yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma ci gaba da dakile shirin siyasa. Kungiyar AU ta bayyana cewa, za ta nemi taimakon kwamitin sulhu na MDD kamar yadda sanarwar da hukumar ci gaban kasa da kasa ta IGAD ta cimma ta tanada a yayin zaman taronta na musammun karo na 28. IGAD, kungiyar kasashen gabashin Afrika da kwamitin sulhu na MDD sun taba bazaranar sanya takunkumi kan banagori daban daban na kasar Sudan ta Kudu dake lalata shirin zaman lafiya. (Maman Ada)