in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Akwai takunkumi ga masu yiwa shirin zaman lafiyar Sudan ta Kudu kafar-ungulu
2015-03-25 10:42:52 cri
Kwamitin sulhun MDD ya fidda wata sanarwar shugaba a jiya Talata, wadda ke nuna matukar damuwa game da gaza cimma yarjejeniyar zaman lafiya, cikin lokacin da aka tsara tsakanin bangarorin Sudan ta Kudu biyu.

Sanarwar ta kuma yi kakkausar suka game da yadda bangarorin biyu ke ci gaba da sabawa yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Kaza lika kwamitin sulhun ya sake jaddada kudurin sa na kakaba takunkumi, ga dukkanin wadanda aka samu suna yiwa shirin wanzar da zaman lafiyar kasar kafar-ungulu.

Cikin sanarwar, kwamitin ya soki shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit, da tsohon mataimakinsa Riek Machar, bisa zarginsu da ci gaba da daukar matakan soja, maimakon warware rikicin kasar ta hanyar siyasa, matakin da ya sabawa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka kulla.

Haka kuma, kwamitin ya jaddada cewa, zai dauki matakai domin sa kaimi ga gwamnati da 'yan adawar kasar, domin su amince da kafa gwamnatin hadin gwiwar al'ummomin kasar, da kuma shimfida yanayin kwanciyar hankali a kasar, tare da tabbatar da gudanar ayyukan jin kai yadda ya kamata a kasar.

A ran 3 ga watan nan da muke ciki ne kwamitin sulhun MDDr ya zartas da kudurin kakaba takunkumi, ga masu haifar da koma baya ga yunkurin zaman lafiya, da na siyasa a kasar Sudan ta Kudu, takunkumin da ya hada da rike kudade da kadarorinsu, da kuma hana su yawon shakatawa a ketare. A sa'i daya kuma, kwamitin zai sake bincike game da yanayin da kasar ke ciki bayan ranar 5 ga watan Maris, da kuma bayan ranar 1 ga watan Afrilu, domin tantance yiwuwar aiwatar da takunkumin hana sufurin makamai cikin kasar da sauran wasu matakai masu alaka da hakan. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China