in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da gasar Olympics ta matasa a birnin Nanjing na kasar Sin
2014-08-17 17:31:09 cri
An gudanar da bikin bude gasar wasannin Olympics ajin matasa ta lokacin zafi karo na 2 a birnin Nanjing dake gabashin kasar Sin.

Bikin wanda ya gudana a ranar Asabar 16 ga watan nan ya samu halartar Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda ya gabatar da jawabin bude gasar. Sauran manyan kusoshin kasa da kasa da suka halarci wannan biki sun hada da shugaban kwamitin Olympics na duniya Thomas Bach, da babban bako na musamman Jacques Rogge, da babban magatakardan MDD mista Ban Ki-moon.

Ya yin wannan kasaitaccen biki, an gabatar da nune-nunen fasahohin al'adu da aka yiwa taken 'samun makoma mai haske', fasahohin da suka kunshi nuna wasu bangarorin al'adun gargajiyar kasar Sin na musamman, da suka hada da bakaken Sinnanci, da kayayyakin tagulla, da na fadi-ka-mutu, da hanyar siliki da ta hada al'ummomin dake yammaci da gabashin duniya a zamanin da, da dai makamantansu.

Baki daya masu nune-nunen fasahohi da masu aikin sa kai fiye da 4000 ne suka nune kwarewar su a wannan biki.

Gasar Olympics ta matasa ta wannan karo ta kunshi wasanni 222, da za a gudanar karkashin manyan fannoni 28, kana 'yan wasa kimanin 3800 na kasashe da yankuna 204, wadanda shekarunsu ke tsakanin 15 zuwa 18 ne suka yi rajistar halartar gasar, inda kasar Sin a nata bangare ta tura wata tawaga mai kunshe da 'yan wasa 123 domin a fafata da su a gasannin da za a gudanar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China