Yau da dare, bisa agogon Beijng, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da bude gasar wasannin Olympics ta matasa ta lokacin zafi karo na biyu a birnin Nanjing na kasar Sin.
'Yan wasa sama da 3700 da suka zo daga kasashe daban-daban ne ake saran za su halarci wasannin guda 222 da za a fafata a kansu, inda za a kashe kwanaki 12 ana yinsu, a sa'i daya kuma, za a gudanar da wasu shirye-shiryen al'adun da abin ya shafa a yayin gasar. Haka kuma, kwamitin gasar wasannin Olympic na kasa da kasa na fatan matasan kasa da kasa za su iya shiga cikin wasannin motsa jiki cikin himma da kwazo, kuma yana fatan matasan kasa da kasa da su iya yin zaman duniya tare da bin akidar Olympic. (Maryam)